Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiNijeriya ce ta biyu da mafi yawan cutar amai da gudawa a...

Nijeriya ce ta biyu da mafi yawan cutar amai da gudawa a Yammaci da Tsakiyar Afirka – UNICEF

Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fama da barkewar cutar amai da gudawa a nahiyar Yammaci da Tsakiyar Afirka, inda ta zo na biyu a jerin ƙasashen da cutar ta fi shafa.

Daraktan yankin Yammacin da Tsakiyar Afirka na UNICEF, Gilles Fagninou, ya bayyana hakan a ranar Laraba, inda ya ce cutar ta zama ruwan dare a Nijeriya, inda take kashe mutane da dama.

Fagninou ya ce, yayin da damina ke ƙaruwa a yankin, yara ne ke cikin haɗari mafi girma, inda akalla yara 80,000 ke cikin haɗarin kamuwa da cutar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata