Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaJam'iyyar Labour Party ta musanta shirin gudanar da zanga-zanga a hedikwatar hukumar...

Jam’iyyar Labour Party ta musanta shirin gudanar da zanga-zanga a hedikwatar hukumar zabe INEC

Jam’iyyar Labour ta nesanta kanta daga zanga-zangar da aka shirya gudanarwa ranar Laraba a hedkwatar hukumar zabe ta kasa INEC, inda ta bayyana wadanda suka shirya ta a matsayin masu son kawo rudanin siyasa.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban rikon jam’iyyar na kasa Ken Asogwa,Sanata Nenadi Usman, jam’iyyar ta ce ba ita ce ta hada wannan zanga-zangar da aka shirya yi ba.

A cewarsa masu shirya zanga-zangar ma ba su san shugabannin jam’iyyar ba, kuma matakin bai samu amincewa da goyon bayan jam’iyyar ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata