Daruruwan masu zanga-zangar da suka haɗa da tsofaffi mata daga ƙauyen Jimrawa da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar lumana a babban birnin jihar, Gusau, kan matsalar rashin tsaro a yankin.
Wannan ya biyo bayan wata zanga-zanga makamanciyar ta a makonni biyu da suka gabata da mazauna ƙaramar hukumar Gusau suka yi, inda suka yi zargin cewa hare-haren ‘yan bindiga sun yi sanadin mutuwar mutane sama da 100 a ƙauyukan da suka haɗa da Mada, Ruwan Bore, Fegin Baza, Lilo da Bangi.
Kaura Namoda da wasu kananan hukumomin jihar Zamfara sun sha fama da hare-hare akai-akai daga ‘yan fashi da makami, inda aka kashe mutane da dama, aka yi garkuwa da wasu, aka lalata dukiyoyi da ababen more rayuwa, sannan ƙauyuka suka zama kufai.
Mazauna yankin sun ce rashin kyawun hanyoyin jihar na taimaka wa ‘yan bindigar, saboda jami’an tsaro na fuskantar ƙalubale sosai wajen isa yankunan da abin ya shafa cikin gaggawa.
