Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiAn cafke wani da ake zargi da sayen ƙuri’a da tsabar kudi...

An cafke wani da ake zargi da sayen ƙuri’a da tsabar kudi Naira miliyan 25.9 a Kaduna

Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna tare da haɗin gwiwar jami’an DSS da sauran jami’an tsaro sun kama wani da ake zargi da niyyar sayen ƙuri’a lokacin zaɓen cike gurbi, tare da kwace kuɗi har naira 25,963,000 hannunsa, a safiyar yau Asabar.

Wanda aka kama, Shehu Aliyu Patangi, an tsare shi da misalin ƙarfe 3:30 na dare a wani otal da ke kan titin Turunku a cikin Kaduna.

A cewar rundunar ’yan sanda, binciken farko ya tabbatar da cewa Patangi ya shirya amfani da kuɗin wajen jan hankalin masu kada ƙuri’a.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Rabiu Muhammad, ta bakin kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya yaba da haɗin kai tsakanin jami’an tsaro, yana mai cewa wannan nasara wani muhimmin mataki ne na tabbatar da sahihancin zaɓe.

Ya gargadi jama’a cewa duk wanda aka kama da hannu wajen karya doka zai fuskanci hukunci, ba tare da la’akari da matsayinsa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata