Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiKotun Kanada ba ta ayyana APC da PDP a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci...

Kotun Kanada ba ta ayyana APC da PDP a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci ba – Binciken Premium Times

Wani binciken jaridar Premium Times ya tabbatar da cewa rahotannin da suka yadu a wasu kafafen yaɗa labarai cewa kotun Kanada ta ayyana jam’iyyun siyasar Nijeriya APC da PDP a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci ba su da tushe.

Binciken ya nuna cewa hukuncin kotun ya shafi wani ɗan siyasa ne kawai mai suna Douglas Egharevba, wanda ya nemi mafaka a ƙasar Kanada.

An ƙi amincewa da bukatarsa ne saboda kasancewarsa ɗan jam’iyyar PDP a wani lokaci da ake zargin jam’iyyar ta yi maguɗin zaɓe da tashin hankali tsakanin shekarar 2000 zuwa 2007.

Kotun ta bayyana cewa PDP ta aikata ayyuka kamar su ƙwace akwatin zaɓe, cusa ƙuri’u, tsoratar da masu kada ƙuri’a da kuma kisan wasu ‘yan adawa a zaɓukan 2003 da 2004. Sai dai kotun ba ta taɓa ayyana jam’iyyar a matsayin ƙungiyar ta’addanci ba.

A cewar binciken, an ambaci APC sau biyar kacal a cikin hukuncin, kuma hakan ya shafi tarihin siyasar wanda ya nemi mafakar.

Binciken ya ce kotun ta yi bayani a fili cewa laifukan da aka tattauna sun shafi PDP kawai, a lokacin da ko ƙirƙiro APC ba a yi ba, domin an kafa ta ne a shekarar 2013.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata