Jam’iyyar APC a jihar Kano ta bayyana damuwa kan abin da ta kira rashin gaskiya da adalci a zabukan cike gurbi na Ghari/Tsanyawa da kuma Bagwai/Shanono da ake gudanarwa.
Shugaban APC na jihar, Abdullahi Abbas, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN a ranar Asabar cewa zaben bai gudana cikin tsafta ba, inda ya nuna damuwa kan yadda ake tsoratar da masu kada kuri’a ga jam’iyyar.
Ya ce magoya bayan APC ana korarsu daga wuraren domin bai wa ‘yan adawa damar yin zabe, inda ya ƙara da cewa ana tura ‘yan daba a yawancin rumfunan zabe suna tsoratar da sauran masu jefa kuri’a na APC.
Abbas ya kuma bayyana cewa har zuwa karfe 11 na safe kayan zabe ba su kai wasu daga cikin rumfunan zabe da ke kananan hukumomin da abin ya shafa ba.
