Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiSERAP ta bukaci EFCC da ICPC su binciki majalisar tarayya kan zargin...

SERAP ta bukaci EFCC da ICPC su binciki majalisar tarayya kan zargin cin hanci na Naira miliyan 3 kafin gabatar da kuduri

Kungiyar da je fafutukar yaki da cin hanci a Nijeriya, SERAP, ta bukaci hukumomin EFCC da ICPC da su binciki majalisun tarayya bisa zargin da wani ɗan majalisar wakilai ya yi cewa ana karɓar kuɗi daga ‘yan majalisa kafin a ba su damar gabatar da kuduri ko korafi.

Ɗan majalisar da ya yi wannan ikirari, Ibrahim Auro, ya bayyana cewa ‘yan majalisa na biyan kuɗi daga Naira miliyan ɗaya zuwa uku, kafin su iya gabatar da kuduri. Ya ƙara da cewa bayan hakan ma sai an ci gaba da lallashin sauran mambobi idan ana so a amince da kudirin.

A wata wasiƙa da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya aike, kungiyar ta bukaci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, su mika batun ga hukumomin yaki da cin hanci domin gudanar da bincike.

SERAP ta ce wannan zargi na cin hanci ya nuna cin amana da karya rantsuwar ‘yan majalisa suka dauka, kuma yana lalata amincewar jama’a da tsarin dokokin kasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata