Uwa kadai ba za ta iya rainon da na miji ya zama cikakken mutum ba sai da taimakon miji- Fitaccen Jarumin Nollywood Jim Iyke

Kalaman fitaccen jarumin fina finan Nollywood Jim Iyke sun jawo cece kuce a shafukan sada zumunta, biyo bayan kalamansa kan cewa uwa kadai ba za ta iya rainon da na miji ta mayar da shi cikakken mutum ba tare da tasirin uba ko wani na miji a rayuwarsa ba.
Jim Iyke ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan rediyon Okay FM da ke Accra Ghana inda yace, mace kadai bata iya bayar da tarbiya ga namiji yadda yakamata.
Ya jadadda cewa ana bukatar tasirin uba ko wani namiji a rayuwar yaron domin ya samu cikakkiyar tarbiyar data dace.
Wannan furuci nasa ya haifar da muhawara a kafafen sada zumunta, inda wasu ke goyon bayan ra’ayinsa kan cewa na miji ya na bukatar jagorancin uba wajen tarbiyar rayuwarsa, yayin da wasu ke kalubalantar maganarsa suna cewa mata da dama sun yi nasarar rainon ya’yansu maza kuma sun yi nasarar kai su mataki mai kyau a rayuwa.
