

Hakan na kunshe ne acikin wani rahoton shekara shekara na gwaje gwajen kwayoyin halittar haihuwa da ake kira DNA da cibiyar Smart DNA Nigeria ta fitar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito
Rahotan ya nuna cewa daga watan Yulin shekarar 2024 zuwa Yuni 2025 yaro 1 cikin 4 na gwajin kwayoyin halitta a Najeriya da aka yi ya nuna iyayyen da suke tare da su ba su ne iyayensu ba.
Binciken ya kuma jaddada cewa matsalar tafi faruwa ga yara na fãri da kusan kaso 64 cikin 100 wadanda ba yaran iyayyen dake rukonsu bane na asali.
