Hukumar tsaron kasar Saudiyya ta kama wata mata ‘yar Kano, Maryam Hussaini-Abdullahi, bayan an ce an haɗa mata da kaya da ba nata ba, wanda aka samu da tabar wiwi cikin jakar “Ghana must go” da aka danganta da sunanta.
Maryam a cewar rahotanni ta tafi Umrah ne tare da mijinta Abdullahi Baffa tun a ranar 6 ga watan Agusta ta jirgin Ethiopian Airlines.
Saidai wannan matsala ta sa mijin nata ya zargin kamfanin jirgin da ƙara musu jaka ba tare da saninsu ba, duk da cewa su biyun sun tafi da jaka ɗaya-ɗaya daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.
Ya ce sun isa Jiddah a ranar 7 ga Agusta bayan sauka a Addis Ababa, kuma sun wuce dukkan matakan bincike ba tare da wata matsala ba, sai daga bisani aka gano matsalar jakar kamar yadda rahoton jaridar Daily Nigerian ya sanar.
