Tuesday, April 7, 2026
HomeSiyasaTinubu na dawo da kwanciyar hankali da fata na gari ga Najeriya...

Tinubu na dawo da kwanciyar hankali da fata na gari ga Najeriya – Ifeanye Okowa

Tsohon gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu na ɗaukar matakai da ke dawo da kwanciyar hankali da fata ga nagari ga ‘yan Najeriya.

Okowa ya yi wannan bayani ne a Abuja, ranar Litinin, yayin taron ƙasa da ƙungiyar Integrity Group of Nigeria (IGN) ta shirya, mai taken “Renew Hope Agenda through Continuity.”

Rahoton jaridar The Nation ya ambato tsohon mai ba shi shawara na musamman kan harkokin majalisar dinkin duniya da majalisar kasa, Pascal Adigwe, inda ya jaddada buƙatar shugaba Tinubu ya ci gaba da jan ragamar mulki domin al’umma su amfana da manufofinsa.

Okowa ya kuma bayyana Tinubu a matsayin wanda ya ɗauki alhakin mulki da girmama nauyin da ya rataya a wuyansa, sabanin wasu shugabannin baya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata