Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiNajeriya na kashe Dalar Amurka biliyan 10 a shekara wajen shigo da...

Najeriya na kashe Dalar Amurka biliyan 10 a shekara wajen shigo da abinci

Ministan Noma na Nijeriya, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana cewa Najeriya na kashe sama da Dalar Amurka biliyan 10 a kowace shekara wajen shigo da kayayyakin abinci kamar shinkafa, alkama, sukari, kifi da ma tumatir.

Sanata Kyari ya bayyana hakan ne a Taron Noma da Fitar da Kayayyaki na First Bank 2025 da aka gudanar a Legas ranar Talata.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito ministan na nuna damuwa da matsalar shigo da kayan abinci, inda ya ce ya zama wajibi a kara zuba jari da tallafi ga manoma don bunkasa harkar noman cikin gida da kuma habaka fitar da kayayyakin gona zuwa kasashen waje.

A cewarsa, duk da cewa noman Najeriya na bada gudunmawar kashi 35% ga GDP tare da daukar kashi 35% na ma’aikata a fannin aikin gona, har yanzu kasar na samun kasa da Dala miliyan 400 daga fitar da kayan gona.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata