Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiShugaban masu rinjaye ya fashe da kuka kan matsalar tsaro a Katsina

Shugaban masu rinjaye ya fashe da kuka kan matsalar tsaro a Katsina

Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Katsina, Ibrahim Umar Dikko, ya fashe da kuka a zauren majalisar yayin da yake bayyana tsananin halin tsaro da ya ta’azzara a ƙaramar hukumar Matazu, inda yake wakilta.

Rahoton jaridar Daily Trust ya ambato Dikko ya ce ‘yan bindiga sun mamaye mafi yawan yankunan mazabarsa, lamarin da ya jefa al’umma cikin tsoro da fargaba, tare da hana manoma shiga gonakinsu.

Ya ƙara da cewa a cikin kwanaki biyu kacal da suka gabata, akalla rayukan manoma 12 aka yi wa sanadi suna aikin gona.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata