Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaMaharan da suka farmaki masallata a Katsina matsorata ne - Faruk Jobe

Maharan da suka farmaki masallata a Katsina matsorata ne – Faruk Jobe

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana ‘yan bindigar da suka kai harin da ya yi ajalin masallata 28 a wani masallaci da ke karamar hukumar Malumfashi a matsayin matsorata.

Mukaddashin gwamnan jihar, Faruq Lawal-Jobe, ne ya bayyana haka a Katsina ranar Asabar, inda ya ce lamarin abin bakin ciki ne kuma abin takaici.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Lawal-Jobe ya yi wannan jawabi ne yayin kaddamar da sabbin motocin yaki guda takwas kirar APC (Armoured Personnel Carriers) da gwamnatin jihar ta saya domin ƙarfafa yaki da ‘yan bindiga.

A ranar Talata, 18 ga Agusta, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari a lokacin sallar asuba a Unguwar Mantau, suka kashe mutane 28.

Saidai rahoton jaridar Daily Nigerian ya ce gwamnatin jihar ta yaba da jarumtar al’ummar da abin ya rutsa da su, domin sun sha kai dauki wajen kare garinsu, abin da ya sa ‘yan bindigar suka dauki matakin kai musu harin ramuwar gayya kenan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata