Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiMatasan yankin Niger Delta sun nemi a cire shugaban NPCL Bayo Ojulare

Matasan yankin Niger Delta sun nemi a cire shugaban NPCL Bayo Ojulare

A safiyar Laraba, wasu gungun shugabannin matasan Niger Delta sun gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin NNPCL a Abuja, inda suka toshe ƙofofin shiga da fita na ginin tun misalin ƙarfe 6 na safe.

Rahotanni da jaridar Punch ta tattaro sun ce masu zanga-zangar dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce suna zargin Shugaban NNPCL, Bashir Ojulari, da cin hanci da rashin iya gudanar da aiki, tare da neman ya yi murabus.

Haka kuma, sun bukaci a nada ɗan asalin yankin Niger Delta a matsayin sabon shugaban kamfanin.

‘Yan sanda da jami’an tsaro sun sun yi dafifi a wurin domin tabbatar da kwanciyar hankali da kuma karkatar da zirga-zirgar ababen hawa zuwa wasu hanyoyin na daban.

An tilasta ma’aikatan kamfanin da dama ajiye motoci a nesa daga ginin saboda toshe hanyoyin shiga da masu zanga-zangar suka haifar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata