Gwamnan Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya amince da naɗin Sanusi Mika’ilu-Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru.
Mai magana da yawun gwamnan, Ahmed Idris, ya bayyana haka a wata sanarwa da aka fitar a Birnin Kebbi a ranar Alhamis.
Jaridar Daily Nigerian ta ambato kwamishinan harkokin kananan hukumomi da masarautu ta jihar, Garba Umar-Dutsin-Mari, na sanar da naɗin, yayin da ya mika takardar tabbatarwa ga sabon sarki a Zuru.
Kwamishinan ya ce daga cikin ƴan takara uku da suka nemi kujerar, bayan kwamitin zaɓen masarautar ya tantance su, Sanusi Mika’ilu-Sami ne ya samu mafi yawan ƙuri’u da suka ba shi damar hawa gadon sarautar Zurun.
An naɗa shi ne sakamakon rasuwar tsohon Sarkin Zuru, Muhammad Sani-Sami Gomo II, wanda ya rasu a ranar 16 ga Agusta, 2025, a wani asibiti da ke Landan.