Sunday, April 5, 2026
HomeKetareTrump ya soke tallafin ketare na dala biliyan 5 a kasafin kudin...

Trump ya soke tallafin ketare na dala biliyan 5 a kasafin kudin Amurka

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ɗauki matakin dakatar da dala biliyan 5 na tallafin ƙasashen waje da majalisar dokokin ƙasar ta riga ta amince da shi, a cewar fadar White House a ranar Juma’a.

Rahoton jaridar Punch ya ce lamarin zai iya ƙara haifar da zazzafar muhawara, yayin da jam’iyyar Democrats ta nuna adawa da wannan mataki.

Trump ya bayyana a cikin wata wasika da ya aike wa majalisar wakilai cewa yanke kuɗin zai shafi shirin Ma’aikatar Harkokin Waje da Hukumar Raya Ƙasashen Waje ta Amurka (USAID).

Tun bayan shiga ofis, gwamnatin Trump ta ke shirin rushe aikin USAID, wadda ita ce cibiyar tallafin ƙetare mafi girma ta Amurka.

Wadda aka kafa ta tun 1961 a zamanin Shugaba John F. Kennedy domin amfani da tallafi wajen jan hankalin ƙasashe masu tasowa a lokacin yaƙin cacar baka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata