DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaban karamar hukuma a Kaduna ya ƙara wa Limamai alawus

-

Shugaban karamar hukumar Soba a jihar Kaduna Muhammad Lawal Shehu, ya bayar da umurnin kara kudin alawus da ake bai wa limaman masallacin juma’a da ke yankin.
Da yake jawabi ga limaman, Honarabul Lawal ya bayyana cewa bayan rantsar da shi ya lura da cewa abin da ake bai wa malamai ba yawa kuma ana shafe tsawon lokaci ba a biya su alawus ba.
Shugaban karamar hukumar ya ce wannan ne yasa ya bayar da umurnin sanya karin wasu limamai cikin tsarin biyan alawus din tare da kara yawan kuɗaɗen da ake biyansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Jam’iyyar ADC ta fara rajista da tantance mambobi na kwanaki 90 a fadin Nijeriya

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta fara shirin rajista, tantancewa da kuma jawo sabbin mambobi na tsawon kwanaki 90 a fadin Nijeriya, domin karfafa jam’iyyar...

Ya kamata a haramta amfani da kafafen sada zumunta ga ’yan kasa da shekara 16 a Nijeriya – Femi Falana

Babban lauya kuma SAN, Femi Falana, ya bukaci a haramta amfani da kafafen sada zumunta ga yara ’yan kasa da shekara 16 a Nijeriya, yana...

Mafi Shahara