Thursday, April 9, 2026
HomeLabaraiNijeriya ta samu lamunin cin bashin dala miliyan $254.76m daga bankin ƙasar...

Nijeriya ta samu lamunin cin bashin dala miliyan $254.76m daga bankin ƙasar Sin domin kammala layin dogo na Kano-Kaduna

Bankin ci gaban ƙasar China ya sanar da bai wa Nijeriya bashin dala miliyan $254.76m domin kammala aikin layin dogo da ya tashi daga Kano zuwa Kaduna.
A cewar wani bayani da bankin ya fitar a ranar Talata, kudaden wata alama ce ta irin kyakkyawar alaƙa da ke tsakanin Nijeriya da China.
A shekarar da ta gabata ne Shugaba Tinubu ya bayar da tabbacin zai kammala aikin layin dogon Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano kuma gwamnati na sa ran kammala na Kaduna zuwa Kano a karshen shekarar 2025.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata