Thursday, April 9, 2026
HomeLabaraiFaransa bata da ikon juya kasashen Afirka - Firaministan Senegal, Ousmane Sanko

Faransa bata da ikon juya kasashen Afirka – Firaministan Senegal, Ousmane Sanko

Ousmane Sanko

Firaministan kasar Senegal Ousmane Sanko, ya caccaki shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, bisa kalaman sa na cewar kasar na bada kariya ga kasashen Afirka.
Wannan dai na a cikin wani sako da Firaministan ya wallafa a shafin sa na Facebook, Ousmane Sanko ya caccaki kasar Faransa da kawo rikice-rikice da dama maimakon cigaban a nahiyar.
Ya kuma zargi Faransa da waragaza kasar Libya wanda hakan ya haddasa tabarbarewar kalubalen tsaro a yankin Sahel.
A baya bayan an alakanta koma bayan karfin ikon da Faransa ke dashi a yankin yammacin Afirka bisa rashin adalci da kulla kakkarfar alaka da kasar Rasha.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata