Hedkwatar tsaron Najeriya ta jaddada cewa dokar shafe shekaru 15 kafin ritaya ga sojojin kasar tana nan.
Wannan ya zo ne bayan da kotun ma’aikata ta kasar da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa dokar ta sabawa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
A cewar kotun, bai kamata a matsawa wani dan kasa ya ci gaba da kasancewa cikin aikin da ba ya ra’ayin sa ba.
Sai dai da yake zantawa da manema labarai a Abuja, daraktan yada labaran hedikwatar Manjo Janar Markus Kangye, ya ce ba za su canja matsaya ba har sai an sauya tsarin dokar aikin sojin a hukumance.
