Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta WAEC ta bayyana tsare-tsaren da ta bullo da su, daidai lokacin da take shirin juya akalar gudanar da jarrabawar ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa a 2026.
Shugaban sashen kula da jarrabawa na hukumar Mr. Lucky Njoagwuani ya bayyana haka ne yayin wani shirin wayar da kai da ya gudana a birnin Fatakwal.
A cewar sa, wajibi ne duk makarantar da za a zana jarrabawar WAEC daga shekara mai zuwa, ta tanadi ingantattun na’urori masu kwakwalwa akalla 250 cikin kyakkyawan tsari.
Kazalika akwai bukatar samar da hasken wutar lantarki da na’urorin sanyi, baya ga kyamarorin tsaro da kuma shiri mai kyau ga masu zana jarrabawa.
Shugaban ya ce daukar wannan mataki zai tabbatar da tsaro yayin jarrabawa da kuma inganta damarmaki.
