Dakarun rundunar sojin Najeriya sun hallaka ’yan ta’adda 15 a jihar Katsina tare da cafke wasu mutum 13 a Kaduna, sannan suka kwato makamai a Benue a wani gagarumin samame daga ranar Juma’a zuwa Asabar.
Majiyar hedikwatar sojin ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa, hare-haren da aka kai ta sama da kasa sun lalata mafakar ’yan ta’adda a yankin Zango, karamar hukumar Kankara, jihar Katsina. Wannan luguden wuta ya yi sanadiyyar mutuwar ’yan ta’adda 15, yayin da wasu da dama suka jikkata.
A jihar Kaduna, jami’an tsaro sun cafke mutane 13 da ake zargi da hannu a aikata miyagun laifuka a Unguwan Dosa, Unguwan Yero, Kwaru da Majalisa, inda aka gano miyagun kwayoyi da wasu abubuwan shaida.
Haka kuma a Sokoto, sojoji sun tarwatsa wani yunkurin ’yan ta’adda a kananan hukumomin Sabon Birni da Wurno, inda suka ceto wani direba tare da motarsa daga hannun maharan.
