Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiMutane 231 sun rasa rayukansu sanadiyar ambaliyar 2025 a  jihohi 25 -...

Mutane 231 sun rasa rayukansu sanadiyar ambaliyar 2025 a  jihohi 25 – Hukumar agaji ta NEMA

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta bayyana cewa ambaliyar ruwa ta shekarar 2025 ta yi ajalin mutane 231 tare da jikkata wasu 607, yayin da aka tabbatar da cewa mutum 114 sun bace.

Rahoton hukumar ya ce jimillar mutane 315,762 ne ambaliyar ta shafa a kananan hukumomi 86 da ke cikin jihohi 25, inda aka ruwaito cewa mutane 113,367 sun rasa matsugunansu, gidaje 40,493 da gonaki 46,304 kuma suka lalace.

NEMA ta fitar da sabuwar kididdigar ambaliyar na 2025 ne a jiya, inda ta bayyana jihohi 10 da aka fi shafa da ambaliyar sun haɗa da:

Lagos: 52,013

Adamawa: 51,713

Akwa Ibom: 46,233

Imo: 29,242

Taraba: 26,722

Rivers: 22,345

Delta: 14,057

Abia: 11,907

Borno: 8,164

Kaduna: 7,334

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata