Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiEl-Rufa'i ya kai karar kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna kan zargin rashin...

El-Rufa’i ya kai karar kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna kan zargin rashin kwarewar aiki

Tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasiru El-rufa’i ya shigar da karar kwamishinan ‘yan sandan jihar gaban hukumar ‘yan sanda ta kasa bisa zargin rashin kwarewa da kuma cin zarafin aiki.

Wannan na zuwa ne bayan da rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta gayyaci tsohon gwamnan tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar hamayya ta ADC, domin amsa tambayoyi da suka shafi batun tayar da zaune tsaye a jihar.

Sai dai cikin karar da ya shigar, Elrufa’i ya bukaci hukumar’ yan sandan ta kasa ta gudanar da cikakken bincike don ganin kwamishinan jihar ya gudanar da aikinsa kan bin tsarin doka da oda, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata