Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaAtiku ya kai ziyarar nuna goyon baya ga Abubakar Malami

Atiku ya kai ziyarar nuna goyon baya ga Abubakar Malami

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya kai ziyara ta musamman ga tsohon ministan shari’a Abubakar Malami, domin jajanta masa bisa harin da aka kai wa ayarin motocinsa a Birnin Kebbi.

Atiku, wanda guda ne daga cikin manyan shugabannin jam’iyyar hadaka ta ADC, ya bayyana damuwa kan yadda ake samun hatsaniya tare da zargin kai wa fitattun jiga-jigan jam’iyyar hari a jihohi daban-daban na ƙasar.

A cikin wata sanarwa da kodinetan shiyya na kungiyar da ke goyon bayan Malami, Muhammad Al-Amin ya fitar, Atiku ya ce ya zama wajibi shugabanni su haɗa kai wajen dakile waɗannan kai hare-hare da suka kira na “adawa da dimokuraɗiyya.”

Ya jaddada cewa jam’iyyar ADC ta ƙuduri aniyar kare ƙasar daga duk wata barazana da ka iya haddasa durƙusar da tsarin dimokuraɗiyya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata