DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rikicin manoma da makiyaya ya yi ajalin mutum 9 a Jigawa

-

Rundunar ‘yansandan jihar Jigawa ta ce mutum 9 ne suka rasa rayukansu biyo bayan wani rikici da ya barke tsakanin Fulani da Makiyaya a yankin Gululu, na karamar hukumar Miga.
Tuni da aka dauko gawarwakin mutanen 9 da suka mutu a yayin fadan da ya tsallaka har zuwa yankin karamar hukumar Jahun.
Jami’an tsaro sun ce rikicin ya tashi ne saboda zargin da wasu manoma ke yi cewa makwabtansu makiyaya sun yi musu sata a shago.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaba Tinubu babbar kyauta ne daga Allah domin gyaran Nijeriya – Yahaya Bello

Tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana shugaban Nijeriya Bola Tinubu a matsayin babbar kyauta da Allah ya ba Nijeriya domin gyaran kasar. Yahaya Bello...

Gwamnatin Nijeriya ta ce cin jarabawar lissafi “Mathematics” wajibi ne ga daliban Sakandare kafin kammalawa

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa lallai dukkan ɗalibai masu rubuta jarabawar kammala sakandare su cigaba da rubuta lissafi tare da harshen Turanci a matsayin wajibi. Mai...

Mafi Shahara