DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
HomeLabaraiMakarantu sama da 180 ne ke rufe a Arewacin Nijeriya sakamakon hare-haren...

Makarantu sama da 180 ne ke rufe a Arewacin Nijeriya sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a cewar wani rahoton jaridar Daily Trust

Wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ya nuna makarantu da yawa a rufe suke yayin da wasu kuma suka koma sansanin ‘yan gudun hijira.

Rahoton ya bayyana akalla akwai makarantu 39 a jihar Zamfara, 30 a Jihar Niger, 6 a jihohin Kaduna da Sakkwato. Sai kuma 52 a jihar Katsina da 55 a jihar Benue.

Sai dai, binciken na Daily Trust bai sanya jihohin Borno, Adamawa da kuma Yobe ba wadanda su ma ke fama da aikace-aikacen ‘yan bindiga tsawo shekaru 15.

Wannan adadi na iya haurawa ko akasin haka sakamakon wasu wuraren ba su shiguwa kamar yadda jaridar ta Daily Trust ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata