Mai ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin tattalin arziki, Dr. Tope Fasua, ya bayyana cewa duk da matsin tattalin arziki da ake fuskanta a halin yanzu, ’yan Nijeriya suna rayuwa mai inganci fiye da shekarun da aka samu ’yancin kai, 1960.
Fasua ya bayyana haka ne a gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, inda ya ce ba daidai ba ne a rika kwatanta yanzu da shekarun baya lokacin samun ‘yancin kai.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta himmatu wajen magance talauci a tsakanin al’umma ta hanyar gyare-gyaren tattalin arziki, saka hannun jari da Samar da ababen more rayuwa ga ‘yan Nijeriya.
