DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeLabaraiDa tabon sace dalibai 'yan mata na Chibok zan mutu - in...

Da tabon sace dalibai ‘yan mata na Chibok zan mutu – in ji Good luck Jonathan

Tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa sace dalibai mata na makarantar sakandiren Chibok da aka yi a shekarar 2014 zai ci gaba da zama tabo a rayuwarsa da mulkinsa har abada.

Jonathan ya yi wannan magana ne a ranar Juma’a a wurin kaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon hafsan tsaron ƙasa, Janar Lucky Irabor, mai taken “SCARS: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum”.

Tsohon shugaban ƙasar ya yaba da irin rawar da Irabor ya taka wajen kare ƙasa, yana mai cewa shi ma’aikaci ne da ya tsaya kan gaskiya ba tare da ya mai da harkokin tsaro zuwa siyasa ba.

Ya ce daya daga cikin manyan tabo a gwamnatinsa shine batun sace ’yan matan Chibok, kuma abin yana damunsa kwarai domin har ya mutu da shi a ransa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata