Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiMatashi ya rasa ransa a gasar daukar siminti da shanye kwalaben giya...

Matashi ya rasa ransa a gasar daukar siminti da shanye kwalaben giya a Nijeriya

Wani faifan bidiyo da ya karade shafukan yanar gizo, ya nuna yadda wani matashi mai suna Gbenga ya rasa ransa sakamakon shiga gasar daukar buhun siminti da yawa a kansa.

 

Jaridar Punch ta ruwaito cewa matashin ya shiga jerin masu son nuna bajinta tsakanin abokansa ne, inda suka sanya gasar daukar buhun siminti biyar a kai.

 

Jaridar ta kuma ce da fari matashin ya dauki buhuna 4 kafin daga baya ya fadi kasa warwas, inda nan take da daina motsi.

 

An dai saka musu gasar ne da nufin bayar da kyautar waya da duk wanda ya lashe.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata