Rundunar sojin kasan Najeriya ta ce ta kama jami’anta 16, bayan samun su da aikata laifukan rashin da’a tare da karya dokokin aiki.
Wata sanarwa da daraktan yada labaran sojin ya fitar, ta bayyana cewa dabi’un da jami’an suka nuna, na da nasaba da rashin samun nasara a jarrabawar karin matsayi a lokuta mabambanta, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
Sanarwar ta ce rundunar ba za ta dauki irin dabi’un nasu ba, kasancewar da dama daga cikin su na da tarihin aikata laifuka a baya.
