Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta ce al’ummar kudu maso yammacin Najeriya ba za su juya wa shugaban Najeriya Bola Tinubu baya a 2027 ba.
Mai magana da yawun jam’iyyar na jihar Seye Oladejo me ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Wannan dai martani ne ga kalaman jam’iyyar adawa ta PDP, wacce ta yi iƙirarin cewa al’ummar wannan yankin ba za su sake zabar Tinubu ba, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
