Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwamnatin jihar Sokoto ta kaddamar da taron jin ra’ayoyin jama’a kan...

Gwamnatin jihar Sokoto ta kaddamar da taron jin ra’ayoyin jama’a kan kasafin kudin 2026

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kaddamar da tarukan jin ra’ayoyin jama’a a mazabu uku na jihar domin shirin kasafin kudin 2026.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, taron da aka gudanar a Tambuwal, Tangaza da Gwadabawa ya haɗa sarakunan gargajiya, ‘yan majalisu, kungiyoyin matasa, mata da masu bukata ta musamman domin tantance bukatun al’umma.

Kwamishinan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Dr. Abubakar Zayyana, ya ce shirin na daga cikin manufar gwamnan jihar, Ahmad Aliyu na tafiyar da mulki a buɗe tare da tafiya da jama’a, wanda zai mayar da hankali kan bangarorin ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa da rage talauci a jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata