Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwamnan jihar Filato ya ba wata mata kyautar Naira miliyan ɗaya saboda...

Gwamnan jihar Filato ya ba wata mata kyautar Naira miliyan ɗaya saboda mayar da dala $5,000 da ta tsinta a Saudiyya

Gwamnan jihar Filato,Caleb Mutfwang, ya bai wa wata mata mai suna Hajiya Zainab Idris kyautar Naira miliyan ɗaya, saboda ta mayar da kuɗin da ta tsinta dala $5,000, a yayin aikin Hajji na bana a Saudiyya.

An bayyana hakan ne lokacin da aka mika mata kuɗin a ofishin hukumar kula da alhazai ta jihar, inda sakataren hukumar, Alhaji Dayyabu Dauda, ya ce gwamnati ta gayyace ta domin nuna godiya da yaba wa irin kyawawan halayenta da ta nuna a ƙasa mai tsarki, tare da tallafa mata da wannan kyauta don ci gaban kasuwancinta.

Dayyabu ya ƙara da cewa, wani mahajjaci mai suna Malam Ayuku ma ya samu kyautar sabuwar wayar hannu daga gwamnati saboda mayar da iPhone da ya tsinta a Saudiyya.

Ya ce gwamnatin jihar tana alfahari da wadannan mutane da suka nuna dattaku da halaye nagari a yayin aikin hajjin da ya gabata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata