Monday, April 6, 2026
HomeKetareMadugun adawar siyasa a kasar Kamaru na samun nasara a wuraren da...

Madugun adawar siyasa a kasar Kamaru na samun nasara a wuraren da Paul Biya ke da karfi a zaben da ke gudana a kasar

Sakamakon da ya fara shigowa daga zaben shugaban kasa na Kamaru ya nuna cewa dan takarar adawa, Issa Tchiroma Bakary, na samun nasara a yankunan da Shugaban Kamaru, Paul Biya ke da karfi a siyasance kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaba Biya mai shekara 92 na fuskantar ‘yan takara tara, ciki har da tsoffin abokansa a gwamnati kamar Bello Bouba Maigari, tsohon ministan yawon bude ido, da kuma Bakary, wanda ya kasance ministan kwadago kafin ya sauka daga mukaminsa.

Biya ya kada kuri’arsa a wata makaranta a birnin Yaoundé, inda ya ki bayyana makomarsa sai bayan an sanar da sakamakon zaben a hukumance.

Rahotanni daga kwamitocin zabe na kananan hukumomi sun nuna cewa jam’iyyar Bakary, FSNC, tana samun nasara a wurare da dama kan jam’iyyar mulki ta CPDM, yayin da wasu majiyoyi suka tabbatar da cewa, Bakary na kan gaba a mazabu da dama a birnin Yaoundé.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata