Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiDantawaye ya zama sabon kwamishinan 'yan sandan Abuja

Dantawaye ya zama sabon kwamishinan ‘yan sandan Abuja

Rundunar ‘yan sanda ta babban birnin tarayya Abuja, ta sanar da fara aikin Dantawaye Miller a matsayin kwamishina na 34 da zai jagoranci rundunar a Abuja.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar a Juma’ar nan, ta ce Miller ya karɓi ragamar ofishin daga tsohon kwamishina Ajao Adewale, wanda ya samu sabon mukami.

A cewar sanarwar, sabon kwamishinan ya yi alkawarin yin aiki tukuru tare da haɗin kai tsakanin rundunar da al’umma domin tabbatar da zaman lafiya a birnin tarayya Abuja.

Rundunar ta kuma roƙi jama’a su ci gaba da ba ‘yan sanda hadin kai wajen yakar muggan laifuka da tabbatar da tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata