DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Custom sun kama haramtattun kayayyaki na sama da miliyan 229 cikin mako guda Ogun

-

Custom sun kama haramtattun kayayyaki na sama da miliyan 229

Hukumar hana fasa kauri ta Nijeriya reshen jihar Ogun, ta yi nasarar kama wasu haramtattun kayayyaki da kudinsu ya kai Naira miliyan 229 da dubu 112 da 424.

Kwanturolan hukumar, Mohammed Shuaibu ne ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin taron tattaunawa da aka gudanar a Idiroko da ke jihar. 

Google search engine

Shuaibu wanda a makon da ya gabata ya kama aiki a jihar matsayin kwantirolan hukumar ya zayyana wasu daga cikin haramtattun kayayyakin da suka kama waɗanda suka hada da buhu dubu 2 da 169 na shinkafa yar waje, da buhunan tabar wiwi dubu 1 da 128 mai nauyin kilogiram dubu 1 da 109 digo 3 da sauran kayayyakin da aka hana shigowa da su Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Atiku ya bukaci karin dauki ga ‘yan kasuwar da iftila’in Singa ya shafa

Madugun adawa a Nijeriiya Atiku Abubakar ya mika sakon jajantawa ga ’yan kasuwa da iyalan da suka yi asarar dukiya a kasuwar Singer da ke...

Saudiyya ta bukaci Musulmi su fara duban jinjirin Ramadan ranar Talata

Babbar Kotun Ƙolin Saudiyya ta bukaci dukkan Musulmi a faɗin Masarautar su fara duban jinjirin watan Ramadan a yammacin ranar Talata, 29 ga Sha’aban 1447AH,...

Mafi Shahara