Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiAbin takaici ne ganin yadda Nijeriya ke cikin kasashen da talauci ya...

Abin takaici ne ganin yadda Nijeriya ke cikin kasashen da talauci ya yi wa lahani – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana talauci a matsayin mafi girman maƙiyi da ɗan Adam ya taɓa sani.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X don tunawa da ranar kawar da talauci ta duniya, Atiku ya ce abin takaici ne ganin cewa Nijeriya na daga cikin ƙasashen da talauci ya fi yi ma lahani.

Atiku ya ce talauci na haifar da cututtuka, jahilci da rashin tsaro, yana mai kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai wajen yaƙi da wannan matsala.

Hakazalika ya kara da cewa dole ne a ɗauki matakai tun daga matakan gwamnati da al’umma domin yaƙar talauci daga gidaje, makarantu da unguwanni.

Daily Trust ta ruwaito yana kara cewa idan talaka ya rasa abin da zai ci, komai yana iya yi domin samun mafita, kuma idan an kawar da talauci, a nan ne ‘yanci da mutuncin ɗan Adam za su samu ma’ana ta gaskiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata