Monday, April 6, 2026
HomeLabarai‘Yan sanda sun kama barawon da ya yi amfani da kakin NYSC...

‘Yan sanda sun kama barawon da ya yi amfani da kakin NYSC don yi fashi a Enugu

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Enugu ta kama wani mutum da ake zargi da yin fashi da makami, ta hanyar basaja da kakin NYSC domin kauce wa binciken jami’an tsaro.

Gidan talabijin na Channels ya ambato sanarwar da mai magana da yawun rundunar, Daniel Ndukwe, ya bayyana a ranar Litinin cewa an kama wanda ake zargi mai suna Chinecherem Ugwuagu, mai shekaru 25, a ranar 11 ga watan Oktoba a kan titin Enugu–Onitsha Expressway.

Ndukwe ya ce jami’an Safer Highway Patrol ne suka cafke shi yayin da yake ƙoƙarin gudu da babur ɗin da ya kwace.

Ndukwe ya tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike kan mutumin, kuma za a gurfanar da shi a kotu da zarar an kammala bincike.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata