Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiMajalisar dokokin Nijeriya na shirin kirkirar sabbin jihohi da kananan hukumomi a...

Majalisar dokokin Nijeriya na shirin kirkirar sabbin jihohi da kananan hukumomi a fadin kasar

Majalisar dokokin tarayyar Nijeriya ta fara tattauna yiwuwar kirkirar sabbin jihohi 55 da kananan hukumomi 278 a fadin kasar.

 

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da hadimin mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Isma’il Mudashir ya fitar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

Sanarwar ta ce tattaunawar wani bangare ne na shirin yi wa kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 kwaskwarima.

 

Ta kuma kara da cewa Sanata Barau I Jibrin, wanda ke jagorantar kwamitin majalisar dattawan kan gyaran kundin tsarin mulki, ya bukaci sauran ‘yan majalisar dokokin da su mayar da hankali wajen kammala yin kwaskwarimar kafin karshen shekarar 2025.

Labari mai alaka: Gwamnan Bauchi ya sanya hannu kan dokar kirkirar sabbin masarautu 13 a fadin jihar

 

Ya bayyana cewa a daidai wannan gaba, akwai kudurori 69 da suka gabatar, bukatar kirkirar sabbin jihohi 55 da kananan hukumomi 278, baya ga yin gyara a iyakokin kasar guda biyu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata