Monday, April 6, 2026
HomeKetareGhana ta sanya dokar fara koyar da yara a makarantu da harshen...

Ghana ta sanya dokar fara koyar da yara a makarantu da harshen uwa

Gwamnatin Ghana ta sanar da sabuwar doka da ta wajabta amfani da harsunan uwa a yayin koyarwa a dukkan makarantun ƙasar, maimakon amfani Turanci.

Ministan Ilimi na ƙasar, Haruna Iddrisu, ya ce wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gyara fasalin tsarin ilimi, domin a cewarsa, yara sun fi fahimtar karatu idan ana koyar da su da harshen da suka fi sabawa da shi.

DW Africa ta ruwaito hukumar Ilimi ta Ghana na cewa za ta sanya idanu matuka wajen ganin an aiwatar da wannan doka a fadin ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata