DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Manyan Jami’an soji za su fuskanci ritayar dole bayan sauye-sauye a fannin tsaron Nijeriya

-

Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai manyan jami’an sojin Nijeriya  masu mukamin Janar akalla 60 da za su fuskanci ritayar dole, biyo bayan sauye-sauyen da shugaba Tinubu ya yi a fannin tsaron kasar.

 

Google search engine

Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda lamarin zai shafa sun kasance a saman sabbin hafsoshin da aka nada a girman matsayin aiki.

 

Majiyoyi sun shaidawa jaridar cewa hakan wani mataki ne na tabbatar da bin ka’idojin aikin soji.

 

Shugaba Tinubu dai ya sauya manyan hafsoshin tsaron Nijeriya ne tare da maye gurbinsu da wasu, lamarin da gwamnati ta bayyana a matsayin wani mataki na karfafa tsaron kasar.

Labari mai alaka: Ka fito ka bayyana wa ‘yan Nijeriya hakikanin dalilin da ya sa ka canza hafsoshin tsaro – Bukatar ADC ga shugaba Tinubu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi ganawar sirri da sabbin hafsoshin tsaro a Abuja

Taron, wanda ya gudana kwanaki uku bayan sanar da sabbin nade-naden, shi ne karo na farko da shugaban kasa ya gana da manyan hafsoshin rundunonin...

Paul Biya ya yi wa masu zanga-zangar sakamakon zabe shagube a Kamaru

Shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya, ya yi shagube ga rikicin siyasar da ke faruwa bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe sakamakon zaɓen shugaban...

Mafi Shahara