Majalisar Dattawan Nijeriya ta shirya fara tantance sabbin hafsoshin tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada, domin tabbatar da su.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar bayan karanta wasikar shugaba Tinubu da ke neman a tabbatar da sabbin shugabannin rundunonin tsaro.
Cikin jerin wadanda za a tantance akwai Janar Olufemi Oluyede, Manjo Janar Waidi Shaibu, Air Vice Marshal Sunday Aneke da Rear Admiral Idi Abbas.
Rahotanni sun nuna cewa za a gudanar da tantancewar a kebance, kamar yadda majalisar ke yawan yi kan batutuwan tsaro, don guje wa bayyanar bayanan sirri na kasa.
Zuwa yanzu rahotanni na nuni da cewa tuni,manyan jami’an suka halarci zauren majalisar domin tantancewar a Larabar nan.
