Kwamitin Ayyuka na Kasa na jam’iyyar PDP ya dakatar da mai ba da shawara kan harkokin shari’a na kasa, Kamaldeen Ajibade (SAN), sakataren jam’iyya na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, mataimakin mai ba da shawara kan shari’a, Okechukwu Osuoha da kuma sakataren shirya taruka na kasa, Umaru Bature, na tsawon wata guda bayan hukuncin kotu da ya dakatar da taron gangamin jam’iyyar da aka shirya.
Jaridar Punch ta ruwaito mai magana da yawun jam’iyyar, Debo Ologunagba, ne ya bayyana haka yayin da yake magana da manema labarai a ranar Asabar, bayan taron gaggawa da kwamitin ya gudanar a ofishin jam’iyyar da ke a Maitama, Abuja.
Ologunagba ya ce kwamitin ya dauki matakin ne bisa tanadin kundin tsarin jam’iyyar, tare da mika wadanda abin ya shafa ga kwamitin ladabtarwa domin daukar matakin da ya dace.
