Biyo bayan barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi na ɗaukar matakin soja kan zargin cin zarafin Kiristoci a Nijeriya, gwamnatin Nijeriya ta ce za ta yi maraba da taimakon Amurka wajen yaƙi da ‘yan ta’adda muddin za a mutunta cikakken ‘yancinta na cikin gida.
Trump ya wallafa a shafinsa cewa ya umurci ma’aikatar tsaron Amurka ta shirya matakin gaggawa idan Nijeriya ta gaza dakatar da kisan Kiristoci, tare da barazanar dakatar da duk wani tallafi kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.
Mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Daniel Bwala, ya ce Nijeriya za ta karɓi duk taimako muddin ana mutunta huruminta, yana mai cewa taron da ake shirin gudanarwa tsakanin Tinubu da Trump zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai kan yaƙi da ta’addanci.
Tun da farko dai, shugaba Bola Tinubu ya musanta zargin wariyar addini, yana mai cewa gwamnatinsa tana aiki tare da shugabannin addinai don tabbatar da tsaro da kare ‘yancin kowane ɗan ƙasa, Musulmi ko Kirista.
