DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An rantsar da shugabar kasar Tanzania, Samia Suluhu

-

Shugabar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta karbi rantsuwa a ranar Litinin bayan zaben da aka yi cikin tashin hankali kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Jam’iyyar adawa ta Chadema ta ce daruruwan mutane sun rasa rayukansu a hannun jami’an tsaro amma hukumar zabe ta bayyana cewa Suluhu ta lashe zaben da kashi 98 cikin dari.

Google search engine

An gudanar da bikin rantsuwar a fadar gwamnati da ke Dodoma ba tare da halartar jama’a ba, yayin da intanet ke a katse gaba ɗaya tun ranar zabe, wanda hakan ya hana samun sahihan bayanai daga kasar.

Wata majiyar diflomasiyya ta ce an samu rahotannin mutuwar mutane da dama a asibitoci, yayin da Chadema ta bayyana cewa sama da mutum 800 ne suka rasa rayukansu, duk da cewa babu tabbacin wannan adadi.

Hukumomin kasar sun musanta zargin amfani da karfin iko, yayin da makarantu da sufuri suka tsaya cak a fadin kasar kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaba Tinubu ya umurci karin jami’an tsaro a jihar Borno biyo bayan harin da aka kai a masallaci – Kashim Shettima

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya ce Gwamnatin Tarayya ta tura ƙarin rundunonin tsaro na musamman zuwa Maiduguri, Jihar Borno, domin kamo waɗanda suka kai...

Kungiyar kwadago ta bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da dokokin harajin da aka gurbata

Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ta bukaci ’yan Nijeriya da su ƙi duk wata dokar haraji da aka ce an sauya ko an yi mata...

Mafi Shahara