Hukumar alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta bayyana cewa ta kammala duba wuraren saukar alhazai da masu samar da abinci a birnin Madina a cikin shirin farkon da take yi na gudanar da aikin hajji na shekarar 2026.
Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban hukumar ta fuskar yada labarai, Ahmad Muazu, ya fitar a ranar Juma’a.
A cewar Muazu, kwamitin ya duba sama da otal 20 da wuraren dafa abinci guda bakwai a yankin markaziyya, inda suka tabbatar da bin ƙa’idojin tsaro, tsafta da sharuddan hukumar.
Hukumar ta NAHCON ta bayyana cewa za ta cigaba da tabbatar da cewa dukkan alhazai daga Nijeriya suna samun ingantaccen ayukka da ya dace da kuɗin da aka biya, tare da ƙarfafa tsare-tsaren da ke tabbatar da gaskiya da inganci wajen hidimomin aikin Hajji.



