Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa ta ayyana tsohon karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, wanda ake nema ruwa-a-jallo bisa zargin hada baki da karkatar da kudade har dala miliyan 14.8.
EFCC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, inda ta ce kudaden sun shafi jarin da hukumar NCDMB ta saka a kamfanin matatar Atlantic International don gina masana’antar sarrafa mai.
Sanarwar, wadda mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale ya sanya wa hannu, ta ce an ayyana neman Sylva ne bayan kotun jihar Legas ta bayar da takardar kama shi a ranar 6 ga watan Nuwamban 2025.
EFCC ta roki duk wanda ke da bayanai game da inda yake ya kai rahoto zuwa ofishin hukumar mafi kusa ko kuma ya sanar da hukumomin tsaro.
