Tsohon babban hafsan sojin kasa kuma tsohon ministan cikin gida na Nijeriya, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau mai ritaya, ya bayyana cewa ’yan bindiga da masu tayar da kayar baya sun mamaye wasu yankunan Arewa, inda suke karɓar haraji tare da kafa dokoki a cikin al’umma.
Dambazau ya bayyana haka ne a taron kafafen yada labarai da tsaro da aka gudanar a Birnin Kebbi, yana mai cewa matsalar tsaro a yankin ta haura shekaru ashirin, inda dubban mutane suka mutu miliyoyi suka rasa matsugunni, manoma da makiyaya kuma suka yi asarar dukiyoyinsu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Dambazau ya bukaci gwamnoni su kafa ma’aikatar albarkatun ma’adinai domin amfani da arzikin kasa wajen habaka tattalin arziki da rage talauci da rashin tsaro.
Haka kuma, ya nemi a farfaɗo da masarautu, a habaka noma, da rage yaran da ba sa zuwa makaranta domin dawo da zaman lafiya a yankin Arewa.
